2 Mayu 2026 - 10:19
Source: ABNA24
Shahada Da Jikkatar Mutane 2 Daga Cikin Dakarun Hashdush -Shaabi A Karbala

Ma'aikatar harkokin cikin gida ta Iraki ta ba da rahoton cewa, sakamakon fashewar wasu burbushin yaki a lardin Karbala, dakarun Al-Hashdush-Shaabi guda 1 ya yi shahada da jikkatar wasu 2

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Ma'aikatar harkokin cikin gida ta Iraki ta ba da rahoton cewa, sakamakon fashewar wasu burbushin yaki a kusa da daya daga cikin rukunin Al-Hashdush-Shaabi a lokacin da suke tabbatar da tsaron hanyar mahajjata ta kasa a lardin Karbala, daya daga cikin dakarun ya yi shahada, wasu biyu kuma suka jikkata.

Kamar yadda Shafaq News ta ruwaito, wannan ma'aikatar ta bayyana cewa, daya daga cikin rukunin Al-Hashdush-Shaabi wanda ke da alhakin tabbatar da tsaro da kariya ga mahajjatan Baiitullah Al-Haram a lardin Karbala, da karfe 6 na daren jiya, a nisan kilomita daya daga wurin da suke, ya fashewar wasu burbushin yaki.

Ma'aikatar ta kara da cewa, nan take wata runduna ta musamman ta aika zuwa wurin da lamarin ya faru, kuma ta dauki matakan da suka dace. Har ila yau, an ce wannan lamari ya kai ga shahadar daya daga cikin dakarun da jikkatar wasu biyu.

A cewar ma'aikatar harkokin cikin gida ta Iraki, an kai wadanda suka jikkata asibitin gundumar Ain Al-Tamur don kula da su.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha